<

Hotunan Jarumi Ali Nuhu tare da Asalin Mahaifansa, Matarsa, da Kuma ‘Yayansa

Hotunan Jarumi Ali Nuhu tare da Asalin Mahaifansa, Matarsa, da Kuma ‘Yayansa

Gwanin Sha’awa Hotunan Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Ali Nuhu Wanda a Yanzu Shine Shugaban Hukumar Finafinai ta Nigeria baki daya.

Mun Kawo Maku Hotunan sa tare da Asalin Mahaifansa, Matarsa , tare da Yayansa guda biyu.

Mahaifin Ali Nuhu

Late Nuhu Poloma

Mahaifiyar Ali Nuhu

Matar Ali Nuhu

Hajiya Maimuna Garba

Yar Gidan Ali Nuhu

Fatima Ali Nuhu

Dan Gidan Ali Nuhu

Ahmad Ali Nuhu

Ali Nuhu Family ❤️

Taron family a Gidan Ali Nuhu

Hajiya Maimuna Garba da Yarta Fatima Ali Nuhu

Hajj. Maimuna Ali Nuhu tare da ‘Ya ‘yanta

CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU

Ali Nuhu An haife shi a ranar 15 ga watan Maris a shekarar 1974 a Jihar Borno. Ya kasance Shahararren jarumin fina-finai, kuma mai shiryawa tare da bayar da umarni na fina-finan Hausa wato Kannywood da Turanci a Najeriya wato Nollywood, Jarumin wanda ake ma lakani da Sarki musamman ma a masana’antar Kannywood.

Shahararre ne a cikin dukkan jarumai na fina-finai musamman na Hausa wato Kannywood, Sarki Ali Nuhu ya yi aure ne a ranar 28 ga watan disamban , shekarar 2003.

Farkon rayuwa

An haifi Ali Nuhu a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.

Ilimi

Ya yi karatu a Jami’ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin fasaha daga Jami’ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami’ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[4]

Sana’ar fim

Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a “Sangaya” wanda ya zama ɗayan finafinan Hausa da suka fi samun kuɗi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal.

Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummawa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana’antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[5]

Related Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

© 2025 Mikiya - WordPress Theme by WPEnjoy